Kungiyar kasashen Larabawa za ta yi taro kan Syria

Taron kungiyar kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron kungiyar kasashen Larabawa

Jami'an kungiyar kasashen Larabawa za su fara tattaunawa a ranar Asabar a birnin Alkahira, domin fayyace irin takunkumin karya tattalin arzikin da za su sanya wa Syria, bayan da ta yi burus da wa'adin da kungiyar ta diba mata na kawo karshen hare-hare kan masu zanga-zangar adawa da gwamnati.

Takunkumin ya hada da hana zirga-zirgar jiragen fasinjan kasar da kuma daina huldar kudi da ita.

Ministan ma'aikatar harkokin wajen Turkiya dai ya ce zai halarci taron, kuma kasar sa za ta goyi bayan kungiyar Larabawan wajen kakaba wa gwamnatin Syria takunkumi.

Duk da cikar wa'adin da kungiyar kasashen Larabawan ta dibarwa Syria, har yanzu jami'ai a kungiyar sun ce kofa a bude ta ke ga kasar kan ta yi biyayya a gare ta.

Sai dai da wuya hakan ya yiwu, ganin cewa tuni gwamnatin Syriar ta bayyana kungiyar da cewa 'yar amshin shatan kasashen yamma ce.

Hari kan sojin Syria

Rundunar sojin Syriar ta tabbatar da cewa, an kashe sojin samanta guda shida, a wani hari da aka kaiwa sansanin sojin da ke garin Homs.

Kakakin rundunar sojin ya ce:'' Wannan hari da aka kai kan kwararrun sojojinmu, wadanda aka bai wa horo kan yaki ta sama- don shirya wa yiwuwar mamaye kasarmu- aikin ta'addanci ne.Ya nuna yadda ake son karya mana lago''.

Rudunar sojin ta zargi kasashen waje da kai harin, kuma ta ce a shirye ta ke ta kare kasar a kowanne hali.

Karin bayani