'Najeriya na kan gaba wajen sare itatuwa'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Wani bincike da kamfanin Maplecroft, wanda ke kula da muhalli, ya wallafa ya nuna cewa Najeriya ce kan gaba a jerin kasashen da ake yawan sare itatuwa a duniya.

Kamfanin ya ce kasar ta yi asarar kasar noma fiye da hekta miliyan biyu daga shekarar 2005 zuwa bara sakamakon yawan sare dazuka.

Kamfanin ya ce binciken da ya gudanar kan kasashe dari da tamanin ya nuna cewa kasashen da suka ci gaba- kamar China da Amurka- basa sare itatuwa da yawa, duk kuwa da kasancewarsu a kan gaba wajen gurbata muhalli.

Wani masani kan muhalli, Alhaji Lawal Funtuwa, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dasa itatuwa don magance zaizayar kasar da sare itatuwa ke jawowa.

Karin bayani