An kai hari kan caji ofis da baki

An kai a Yobe Hakkin mallakar hoto 1
Image caption An kai hari a Yobe

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewa wasu mutanen da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari kan wani caji ofis da kuma banki a garin Geidam dake jihar Yobe.

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da al'amrin.

A lokacin da BBC ta tuntubi kwamishinan 'yan sanda na jihar ya ce ba shi da uzurin yin magana, saidai da muka kira shi daga bisani, wayarsa bata shiga.

Sai dai a hirar da muka yi da wani mazaunin garin wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya bayyana cewa an samu tashin bam baya ga harbe harben bindiga.