Amurka ta nemi gafara a wajen Pakistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hillary Clinton

Kasar Amurka ta nemi gafara daga wajen Pakistan bayan dakarunta sun kashe sojojin Pakistan ashirin da biyar a kan iyakar kasar da Afghanistan a ranar Asabar.

Wata sanarwa ta hadin gwiwa da sakataren tsaron kasar, Leon Panetta da takwararsa ta harkokin waje, Hillary Clinton, suka fitar ta bayyana alhinin gwamnatin Amurka ga iyalan sojojin da aka kashe a harin da dakarun NATO suka kai a kasar.

Sanarwar ta ce Amurka za ta gudanar da cikakken bincike game da batun, tana mai cewa ba da gayya aka kai harin ba.

Da alama matakin da Pakisan ta dauka na sake nazarin dangantakar da ke tsakaninta da Amurka ya firgita Amurkan, wacce ba ta yi wata-wata ba, wajen neman gafara daga hukumomin Pakistan din.

Matakan da Pakistan ta dauka

Ita dai Pakistan ta dauki matakai ne wadanda suka hada da daina musayar bayanan sirri tsakaninta da Amurka , da rufe iyakarta da Afghanistan, kana ta nemi Amurka da ta janye sojojinta daga sansanin sojin saman kasar da ke Baluchistan cikin kwanaki goma sha biyar.

Idan Pakistan ta aiwatar da wadannan mataki, hakan zai yi mummunan tasiri game da yakin da Amurka ke yi da masu tayar da kayar baya a kasar.

Gafarar da Amurkan ta nema dai, wata hanya ce ta sassauta fushin da Pakistan ta yi, sai dai har yanzu Pakistan din ba ta ce uffan game da kalaman Amurkan ba.

Karin bayani