Zabe a Masar: Ba gudu ba ja da baya

Field Marshall Hussein Tantawi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban majalisar sojojin kasar Masar

Shugaban majalisar mulkin sojin kasar Masar ya ce za a gudanar da zaben shugaban majalisar dokoki a gobe, Idan Allah Ya kai mu, kamar yadda aka tsara,duk kuwa da karuwar tashin hankalin siyasa da ake samu a kasar.

Feild Marshall Hussein Tantawi ya ce ba zai kyale duk wata kungiya ta nemi sa matsin lamba a kan rundunar sojin kasr ba.

Ya kuma bukaci manyan 'yan takarar shugabancin kasar biyu, Muhammad el Baradei, da Amr Moussa da su goyi bayan mutumin da ya nada praminista cikin makon jiya.

Masu zanga zanga sun nemi a yi wani babban gangami a yau din nan, kamar yadda daya daga cikinsu Hiba Hani, ke cewa, muna kokarin kafa gwamnati ne da zata kare bukatun da suka sa mu juyin juyahali.

Ba ma goyon bayan sabon praminsta, Kamal Ganzoury.

Karin bayani