Kotun Duniya ta ICC ta mika wa Laurent Gbabo sammace

Tambarin kotun Duniya ta ICC Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambarin kotun Duniya ta ICC

Lauyoyin tsohon shugaban Cote d'Ivoire, Laurent Gbagbo, sun ce kotun duniya mai shari'ar mugayen laifuka, ta bada sammacin kama shi.

Kotun duniyar dai bata tabbatar da hakan ba.

A watan Afrilun da ya wuce ne aka tunbuke shugaba Gbagbon, bayan an dan yi yakin basasa, saboda ya ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar na shekarar da ta wuce.

Tun lokacin da aka kawar da Laurent Gbagbon daga mulkin ake tsare da shi a wani gida, a arewacin kasar ta Cote d'Ivoire.

An zargi dakarunsa da kashe abokan hamayyar siyasa da kuma fararen hula, bayan zaben shugaban kasar na bara, wanda Alassane Ouattara ya lashe.

Karin bayani