Birtaniya ta gargadi Iran game da abinda ka- je ya- dawo

Masu zanga zanga kan Birtaniya a Iran Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu zanga zanga kan Birtaniya a Iran

A Iran, masu zanga zangar nuna adawa da takunkumin da Birtaniya ta sa wa kasar, sun kutsa kai cikin ofishin jakadancin Birtaniyar, da kuma wani ginin na dabam, mallakar ofishin jakadancin, a Tehran, babban birnin kasar.

Masu zanga zangar sun yage tutar Birtaniya da ke kofar shiga ofishin jakadancin, suka kuma farfasa tagogi, tare da yin watsi da takardu.

Daga baya dai 'yan sanda sun samu sun ciyo kan lamarin.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague, ya ce ko kadan bai dauki abinda ya farun da wasa ba.

Ya ce, rashin sanin ciwon kai ne, kuma gwamnatin Iran ce da laifi.

A nata bangaren, ma'aikatar harkokin wajen Iran ta yi nadamar abinda ta kira: halayyar masu zanga zanga, wadda ba za a amince da ita ba.

An yi zanga zangar ne a wurare biyu a gine ginen Diplomasiyyar Birtaniya dake birnin Tehran.

Na farko an yi shi ne a katafaren ofishin jakadancin dake tsakiyar babban birnin, inda hotunan da aka dauko daga can ke nuna tarin masu zanga zangar sun hau kan babban kyauren ofishin jakadancin.

Sun kone Tutar Birtaniya, da tambarin kasar, sannan kuma sun juya hoton Sarauniyar Ingila sama a kasa.

Sannan ma rahotanni na bayyana cewa masu zanga zangar sun dirarwa wani ginin jakadancin Birtaniyan dake arewacin birnin Tehran.

Tuni dai ofishin dake kula da harkokin wajen Birtaniyan yayi Allah Wadai da wannan al'amari, yana mai cewa sun yi magana da ofishin dake kula da al'amuran Iran a London kan yayi kira ga Jami'an Iran da su dauki matakin gaggawa domin tabbatar da lamarin bai wuce ikon su ba.

Sannan kuma ma ofishin dake kula da harkokin wajen na Birtaniyan ya nemi da 'yan Birtaniyan dake zaune a Iran da su zauna a cikin gidajensu, domin kada su fiye bayyana kansu ga masu zanga zangar.

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da Birtaniya ta kakabawa Iran takunkumi ta bangaren da ya shafi hada hadar kudade. Inda ita kuma Iran ta mayar da martanin alkawarin sallamar Jakadan Birtaniya dake kasar ta.

Ga wadansu da dama dai, wannan na tuna musu abubuwa makamantan wannan da suka faru a shekarar 1979 wadansu dalibai sun dirarwa ofishin jakadancin Amurka dake Tehran, tare da tsare wasu jami'an diplomasiyyar kasar tsawon fiye da kwanaki dari hudu.

Karin bayani