Boko Haram za ta iya kaiwa Amurka hari - 'Yan Majalisa

Motocin da aka kona a harin Boko Haram Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani rahoton da kwamitin tsaron cikin gida na majalisar wakilan Amurka mai kula da yaki da ta'addanci ya wallafa a yau, ya ce kungiyar nan ta Jama'atu Ahlus - sunna Liddawati Wal Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram a Najeriya, na iya kai wa Amurka hari har gida idan ba a dauki mataki ba.

Rahoton mai shafi talatin wanda wasu 'yan majalisar wakilan Amurkan biyu suka wallafa, ya ce jami'an leken asirin Amurka suna kuskure wajen tunanin cewa kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda ba za su iya kai wa Amurka hari har a gida ba.

A baya dai kungiyar ta Boko Haram ta yi ikirarin kai hari kan ofishin majalisar dinkin duniya dake Abuja babban birnin Najeriyar, batun da 'yan majalisar wakilan Amurkan suka ce yana nuni da cewa ta yiwu kungiyar za ta fadada kai hare-harenta kan wasu cibiyoyin kasashen yammacin duniya.

Rahoton wanda 'yan majalisar wakilan Amurka Patrick Meehan da Jackie Speir suka wallafa, ya nuna cewa harin da 'yan kungiyar Boko Haram, suka kai a kan ofishin majalisar dinkin Duniya da ke Abuja ranar 26 ga watan Agustan da ya gabata, shi ne ya nuna gagarumin sauyi a manufar kungiyar, wadda a baya ta takaita kai hare-harenta kan cibiyoyin Najeriya.

Rahoton ya ce duk da cewa an kai harin ne a cikin Najeriya, amma shi ne na farko a kan wata cibiya da ba ta gwamnatin Najeriya ba, hakan ya karkato da hankalin jami'an leken asirin Amurkan kan kungiyar wadda a baya suke da karancin masaniya kan aikace-aikacenta.

'Yan majalisar wakilan Amurkan sun kuma ce wani sakon bidiyo da ya fito daga kungiyar ta Boko Haram makwanni bayan harin, ya ambato wani mai magana da yawun kungiyar yana bayyana majalisar dinkin duniya a matsayin matattarar shedanci ta duniya, kuma sun kai harin ne domin su aike da sakon gargadi ga shugaban Amurka Barack Obama da kuma sauran makiya addinin musulunci.

Rahoton ya kuma ambato wani babban jami'in rundunar tsaron Amurka mai sa ido kan nahiyar Africa wato Africom yana cewa, bayanan da suka tattaro, sun nuna cewa 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram suna samun horo daga 'yan kungiyar Al-qaeda a yankim Maghrib.

Har wayau akwai bayanan da ke nuna cewa suna da alaka da kungiyar Al-Shabab ta Somaliya abin da ya sa a yanzu jami'an leken asiri na Amurka suka nuna damuwa a kan cewa akwai yiwuwar kungiyar za ta iya kai hare-hare a kan wasu cibiyoyin kasashen waje da ke Najeriya, da nahiyar Afrika da ma uwa uba kai wa ita kanta Amurkan hari har gida.

'Yan majailsar wakilan na Amurka sun ce, a baya an yi tsammanin kungiyoyi irinsu Alqaeda a yankin larabawa da da kuma Teriki Taliban da ke Pakistan ba za su iya kai hare-hare a kan Amurka ba.

Amma hare-haren da suka shirya na dan Najeriyan nan da ake zargin ya yi yunkurin kai hari ranar kirsimeti a shekarar 2009 da kuma wanda aka yi yunkurin kai wa a Times Square a watan Mayun shekarar 2010, sun nuna cewa bai kamata a raina irin illa da kungiyar Boko Haram ka iya yi ba duk kuwa da karancin kwarewar da wasu ke ganin suna da ita.

A don haka rahoton na 'yan majalisar wakilan ya yi kira ga gwamnatin Amurka da kada ta raina karfin kungiyar ta Boko Haram na kai mata hare-hare har gida, sannan kuma ta yanke shawara ko za a bayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta'addanci ta duniya.

Rahoton ya kuma yi kira ga hukumomin leken asirin Amurka da su kara kaimi wajen tattaro bayanai a kan kungiyar ta Boko Haram, ta kuma tattauna da 'yan Najeriya da ke zaune a Amurka domin samun karin bayanai a kan ko su waye 'yan boko haram, sannan kuma a kara tallafin da ake baiwa gwamnatin Najeriya a yakin da take yi da ta'addanci.

Sai dai rahoton ya ce, har yanzu wasu manyan jami'an sojin Najeriya ba su dauki hadarin da Boko Haram ke dauke da shi da muhimmanci ba, domin sojojin da aka tura don dakile hare-haren kungiyar wasunsu ba a biyansu hakkokinsu a kan kari.

Rahoton ya kuma yi kira ga Amurka da ta kara kaimi a alakarta da al'ummomin Musulmi da ke arewacin kasar.

Karin bayani