Yajin aiki mafi girma a Burtaniya

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ma'aikata a Burtaniya za su gudanar da yajin aiki mafi girma cikin shekaru goma

Burtaniya na fuskantar yajin aiki mafi girma cikin shekaru fiye da goma a yau.

Akalla ma'aikata miliyan biyu ne za su nuna fushinsu kan yunkurin da gwamnatin Kasar ke yi wajen gudanar da wasu sauye-sauye a shirin fansho na Kasar.

Ana sa ran za a samu tsaiko matuka a harkoki, saboda kungiyoyi kamar na malaman makaranta da na ma'aikatan asibiti da na hukumar shige da fice ba za su je aiki ba.

Lamarin zai tilasta rufe makarantu tare da kawo hargitsi a filayen jiragen sama.

Ma'aikatan gwamnati sun ce an bukaci su yi aiki fiye da yadda suka saba, sannan kuma a karshe su samu kudin fanshon da bai taka-kara-ya-karya ba.

Amma gwamnatin Kasar ta ce zata samar da karin guraben ayyuka fiye da wadanda kamfanoni masu zaman kansa ke samarwa.

Karin bayani