Birtaniya ta kori jakadan kasar Iran

Ofishin jakadancin Iran a London Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ofishin jakadancin Iran a London

Gwamnatin Birtaniya ta bada umurnin a rufe ofishin jakadancin Iran da ke nan London, kuma ta ce dole ma'aikatan ofishin jakadancin su bar kasar nan da sa'o'i arba'in da takwas.

Sakataren harkokin wajen Birtaniyar ne, William Hague ya bada sanarwar, kwana daya bayan da masu zanga zanga a birnin Tehran, suka afkawa ofishin jakadancin Birtaniya da ke can, da kuma wani ginin na dabam, mallakar ofishin jakadancin.

Mista Hague ya ce, hakan ba zai faru ba, ba tare da sanin hukumomin Iran ba, ko da yaya ne.

Inda ya ce, duk wata kasar da ta hana su gudanar da aikinsu kamar yadda ya kamata a kasarta, kada ta sa ran cewa za su bar ofishin jakadancinta a kasarsu ya yi aikinsa kamar yadda ya dace.

William Hague ya ce, a yanzu Birtaniya ta rufe ofishin jakadancinta a Tehran, kuma ta kwashe ma'aikatanta.

Wani kakakin gwamnatin Iran ya ce, Birtaniya ta yi gaggawar maida murtani, amma ta kwan da sanin cewa, Iran za ta kara daukar matakan da suka dace.

Karin bayani