Kudirin kyautata aikin jarida a Nijar

Shugaba Mahamadou Issoufou
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar yau ne shugaban kasar Alhaji Isufu Mahamadu ya rattaba hannu a kan wata sanarwa da ta kunshi matakan kare hakkin 'yan jarida.

'Yan jaridar kasar ta Nijar ne dai suka suka gabatar ma shi da kundin a karkashin wani kampe da kungiyoyin 'yan jarida na duniya suka kaddamar game da yaki da hukuncin tsare dan jarida a gidan kaso bisa aikata kura-kurai a cikin ayyukansa.

A lokacin yakin neman zabe ne dai shugaban na Nijar ya yi alkawarin sa hannu a kan wannan kundin, muddin ya zama shugaban kasa.

Masu sharhi kan al'ammuran yau da kullum dai na ganin cewa cimma wannan mataki, wani ci gaba ne a kasar, saboda ko a shekara ta dubu 2 da 10 gwamnati ta zartas da dokar hana kulle dan jarida a gidan yari.

Karin bayani