Ma'aikata sun kauracewa aiki a Burtaniya

Ma'aikatan da ke yajin aiki
Image caption Zanga-zanga daban-daban har 1,000 ma'aikata ke yi

Ma'aikatan gwamnati a Burtaniya sun kauracewa wuraren aikinsu don nuna rashin amincewa da tsarin fansho a abin da kungiyoyin kwadago suka kira yajin aiki mafi girma a shekaru da dama.

Daga cikin wuraren da abin ya shafa akwai makarantu, da asibitoci, da filayen jiragen sama, da tashoshin jiragen ruwa, da ofisoshin gwamnati a fadin kasar, inda ake zanga-zanga daban-daban har guda dubu daya.

Ministan kudi na Burtaniyar ya yi kira a kara tattaunawa, yana mai cewa yajin aiki ba zai haifar da komai ba.

Su dai kungiyoyin na kwadago suna adawa ne da shirin gwamnati na kara yawan gudnmawar da mambobinsu za su bayar ga asusun fansho da kuma kara shekarun da zu kwashe suna aiki kafin su samu fanshon.

  • A cewar mai aikowa BBC rahotanni a bangaren ilimi, Gillian Hargreaves, kusan makarantu 2,700 ne a cikin makarantu 21,700 a Ingila ke bude
  • Ma'aikatar Ilimi ta ce tana sa ran kashi goma sha uku cikin dari na makarantun Ingila ne za su bude; kashi goma sha uku kuma za su bude amma ba za su yi aiki ba. Ba a san halin da kashi goma sha shida cikin dari ke ciki ba
  • Lamarin bai sahafi akasarin jiragen saman da ke sauka da tashi a manyan filayen jiragen saman Burtaniya biyu--Heathrow da Gatwick--ba; saukar jirage kalilan aka soke
  • A arewacin Ireland, babu motar safa ko jirgin kasan da zai yi aiki, kuma kashi biyu cikin uku na makarantu da kwalejoji ba za su bude ba.
  • Kungiyoin kwadago sun kiysta cewa ma'aikatan gwamnati 300,000 ne ke yajin aiki a Scotland yayin da ma'aikata 170,000 suka bi sahu a Wales
  • A Ingila, gwamnati ta kiyasta cewa nas-nas da ma'aikatan lafiya da sauran ma'aikatan asibiti, ciki har da masu shara da akantoci 400,000 za su shiga yajin aikin. Ta kuma ce an dakatar da gwaje-gawaje da ganin likita na marasa lafiya 60,000
  • A Scotland, akalla ayyukan asibiti 3,000 abin ya shafa
  • Kungiyoyin kwadago sun ce ko da ya ke ma'aikatan kotu za su shiga yajin aikin, al'amarin ba zai shafi shari'ar wasu mutane biyu ba wadanda ake zargi da kisan wani matashi mai suna Stephen Lawrence

Kungiyoyin kwadago sun ce kusan ma'aikatan gwamnati miliyan biyu ne suka shiga yajin aikin.

Daga Brussels, Ministan Kudi George Osborne ya shaidawa BBC cewa: "Ba abin da wannan yajin aiki zai haifar; ba zai kuma sauya komai ba, sai dai ma ya kara raunana tattalin arzikinmu ya kuma jawo asarar ayyuka.

"don haka ya kamata mu koma kan teburin shawarwari, mu cimma matsaya a kan tsarin fanshon da ya dace da ma'aikatan gwamnati, wanda kuma gwamnati za ta iya biya.

"abin da ya kamata a ce muna yi ke nan yau, ba yajin aiki ba".

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan Kudi na Burtaniya, George Osborne

Ya kuma kara da cewa idan ba a runtsa ido an dauki matakai masu zafi ba, tattalin arzikin kasar zai durkushe.

Shugaban jam'iyyar adawa ta Labour, Ed Miliband, ya ce yana tausayawa mutanen da yajin aikin ya kuntatawa.

Sai dai kuma ya ce ba zai yi Allah-wadai da ma'aikatan da suka yanke shawarar tafiya yajin aikin ba saboda suna tunanin gwamnati ta kai su bango.

Mai kula da al'amuran baitul mali a jam'iyyar Labour, Rachel Reeves, ta shaidawa BBC cewa jam'iyyarsu ba ta goyi bayan yajin aikin ba.

"Ba ma goyon bayan yajin aikin saboda yajin aiki alama ce ta gazawa", in ji ta.

Babban sakataren kungiyar kwadago ta Unison, Dave Prentis, ya shaidawa BBC cewa da wuya a ga kungiyarsa ta shiga yajin aiki, to amma ma'aikatan gwamnati sun fusata.

A cewarsa, gwamnati ba ta yin adalci ga miliyoyin ma'aikata, akasarinsu kuma mata masu karancin albashi.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mambobin kungiyar kwadago ta Unison

"A lokacin ne mutane za su ce ya isa haka", in ji shi.

Shi kuwa babban sakataren TUC, Brendan Barber, ya ce ma'aikatan gwamnati na fuskantar hari na babu gaira babu dalili daga gwamnati.

Ana dai sa ran yajin aikin na sa'o'i ashirin da hudu zai kawo tsaiko a ayyukan kotuna, da cibiyoyin daukar ma'aikata, da kananan hukumomi, da dakunan karatu, da ma aikin kwashe shara.

Sakataren Ilimi, Michael Gove, ya ce ba a yi adalci ba idan bukaci masu biyan haraji su dauki nauyin dimbin kudaden 'yan fansho.

Karin bayani