Batutuwan da aka fi tattaunawa a duniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tambayi mutane 11,293 a kasashe 23 batutuwan da suka tattauna a kansu, su da abokansu ko iyalansu

Abubuwa da dama ne dai wadanda kafofin yada labarai ke bayar da rahotanni a kansu ka iya jefa jama'a cikin damuwa, kama daga matsalalolin kudi a kasashen da ke amfani da kudin euro zuwa karuwar yawan aikata manyan laififfuka, ko ma sauyin yanayi.

To amma wadanne batutuwa ne, takamaimai, mutane a fadin duniya suka dugunzuma a kansu? Sannan kuma wadannan abubuwan da ke damun mutane yanzu su ne suke damunsu ko kuma suka tattauna a kansu da abokansu a 'yan shekarun da suka gabata?

Wadannan tambayoyi ne masu kayatarwa, sai dai kuma babu amsoshi takamaimai.

To amma na baya-bayan nan a jerin kuri'un jin ra'ayin jama'a da Sashen Yada Labarai ga Kasashen Duniya na BBC—wato BBC World Service—ya sa a gudanar duk shekara, wanda ake kira The World Speaks, ya dan leko muhimman batutuwan da ke kai-komo a zukatan mutane.

Yayin kuri'ar jin ra'ayin jama'ar, an gabatarwa mutane dubu goma sha daya da dari biyu da casa'in da uku a kasashe ashirin da uku wadansu jerin batutuwan da suka shafi duniya, aka kuma nemi su bayyana batutuwan da suka tattauna a kansu (a cikin batutuwan da aka gabatar) su da abokansu ko iyalansu a cikin wata guda kafin lokacin kuri'ar jin ra'ayin jama'ar.

An kuma bukace su ta hanyoyi da dama su bayyana batutuwan da suke ganin suna da muhimmanci a binciken da kamfanin shirya kuri'ar jin ra'ayin jama'a na GlobeScan ya gudanar a madadin BBC.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Binciken ya gano cewa mutane sun tattauna batun cin hanci da rashawa fiye da komai a duniya. Kusan rubu'i, wato kashi ashirin da hudu cikin dari, na wadanda aka tambaya, sun tattauna batun a cikin wata guda kafin loakcin.

Daga nan sai batun matsanancin talauci ko fatara. Kashi ashirin cikin dari, ko kuma daya bisa biyar na mutanen da aka tuntuba, sun ce sun tattauna batun ba da jimawa ba. Rashin aikin-yi da batutuwan da suka danganci hauhawar farashin kayayyaki, misali tsadar abinci da makamashi, sun yi kankankan a matsayi na uku.

Kashi goma sha takwas cikin dari na wadanda aka tambaya ne dai suka ambaci batutuwan guda biyu.

Sai dai kuma rashin aikin-yi ne batun da damuwa a kansa ke karuwa cikin hanzari fiye da sauran batutuwan. Yawan mutanen da aka tambaya a dukkan kasashen da aka duba wadanda suka ce sun tattauna batun rashin aikin-yi su da abokansu ko iyalansu a cikin wata guda kafin lokacin ya rubanya yawan wadanda suka fadi hakan yayin kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta shekarar 2009 har sau shida.

Yawan nuna damuwa a kan wannan batu dai ya bambanta daga kasa zuwa kasa. Inda aka fi nuna damuwar dai a Spain ne, inda kashi hamsin da hudu cikin dari na wadanda aka tambaya suka ce sun tattauna batun rashin aikin-yi ba da jimawa ba; wannan adadi kuwa ya rubanya na wadanda suka nuna irin wannan damuwa a kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta bara. Spain dai ta yi dumu-dumu a cikin matsalar bashin da ta addabi kasashe masu amfani da kudin euro; kuma yawan marasa aikin-yi a kasar ya yi tashin gwauron zabi.

Sauran kasashen da aka fi nuna damuwa a kan wannan batu sun hada da Ghana, da Mexico, da Najeriya, da Turkiyya; adadin wadanda suka ce sun tattauna batun a cikin wata guda kafin lokacin ya kai sulusin mutanen da aka tambaya.

Za a iya hasashen cewa karuwar damuwa dangane da rashin aikin-yi yana da alaka da matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta yanzu haka, kamar matsalar kudaden da ta addabi kasashe masu amfani da kudin euro da kuma jan kafar da ya biyo baya a bunkasar tattalin arzikin manyan kasashen duniya.

Sai dai babu tabbas a kan hakan. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta farko wadda aka wallafa a shekarar 2009 ta zo ne a daidai lokacin koma-bayan tattalin arzikin da ya fi na yanzu wanda ke da alaka da durkushewar bankin saka-jarin nan na Amurka, wato Lehman Brothers.

Cin hanci da rashawa da kuma fatara sun ci gaba da bayyana a jerin batutuwan da aka fi tattaunawa a duniya. Kuri'un jin ra'ayin jama'a ukun da aka gudanar ya zuwa yanzu sun nuna cewa wadannan batutuwa ne a kan gaba.

Amma fa sakamako na baya-bayan nan ya nuna wagegen gibi a tsakanin kasashe dangane da batutuwan da mutane ke ganin sun fi muhimmanci. A Amurka, da Faransa, da Japan, wadanda dukkaninsu kasashe ne da suka ci gaba, an fi tattauna halin da tattalin arzikin duniya ke ciki fiye da kowanne batu.

Sabanin haka kuwa, a Najeriya, da Turkiyya, da Indonesia, da Peru, an fi tattauna batun cin hanci da rashawa ne.

Daukacin wadannan kasashe dai masu tasowa ne, wadanda kuma suka yi kaurin suna wajen cuwa-cuwa a ayyukan gwamnati da ma harkar kasuwanci. A wani rukunin na kasashe masu tasowa wadanda suka hada da China, da Rasha, da Kenya, da Philippines kuwa, tsadar abinci da ta makamashi su ne manyan batutuwan da aka fi tattaunawa.

Amma a Latin Amurka, miyagun laifuffuka da tashe-tashen hankula aka fi tattaunawa. Hasali ma dai a Brazil, kasar da ta yi kaurin suna wajen zaman dardar a unguwannin marasa galihu, da Ecuador, da Mexico, kasar da ta shahara a kashe-kashe masu alaka da fataucin miyagun kwayoyi, miyagun laifuffuka da tashe-tashen hankula ne suka fi jan hankalin masu tattaunawa.

Hakkin mallakar hoto globescan
Image caption Kamfanin Globescan ne ya gudanar da binciken a madadin BBC

Ga alama mutanen da ke kasashen da suka ci gaba suna damuwa da tasirin da sauyin yanayi zai yi nan gaba fiye da mutanen da aka tambaya a matalautan kasashe masu tasowa.

Amma kusan a ko'ina batun dumamar yanayi ya fado kasa a jerin batutuwan da aka tattauna a cikin wata guda kafin lokacin gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'ar. A bara wannan batu aka tattauna fiye da kowanne a kasashe goma, amma batun na kan gaba ne a bana a kasashen Jamus da Burtniya kawai.

Kamfanin Globescan ya yi aikin tattaro bayanai a kuri'ar jin ra'ayin jama'ar ta baya-bayan nan ne a madadin BBC a tsakanin watan Yuli da watan Satumba na bana.

Labaran BBC