Amnesty ta nemi a kama George W Bush

George W Bush Hakkin mallakar hoto AP
Image caption George W Bush

Kungiyar kare hakkin bil -adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Ethiopia, da Tanzania, da kuma Zambia da su kama tsohon shugaban Amurka George Bush a lokacin ziyarar da ake sa ran zai kai kasashen tsakanin ranar daya zuwa biyar ga watan Disamba.

Kungiyar ta Amnesty ta bukaci da a tsare shi kan laifukkan da ake zargin ya aikata na cin zarafin biladama a karkashin dokokin kasashen duniya.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da ta aike wa manema labarai.

Ana zargin George W Bush ne da bada umurnin a kai hari kan wasu kasashe masu 'yanci, kamar Iraki da Afghanistan.

Tsohon shugaban Amurkar, zai kai ziyarar ne, kan batun yaki da sankarar mahaifa.