'Yan adawa sun kulla 'yarjejeniya

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Babbar jam'iyyar adawa ta kasar Syria, wato Syrian National Council ta ce ta cimma yarjejeniya da kungiyar masu tada kayar baya ta Free Syrian Army domin rage hare- haren da suke kaiwa kan dakarun gwamnatin kasar.

'Yarjejeniyar ta biyo bayan taron farko da shugabannin bangarorin biyu suka yi a kudancin Turkiyya.

An dai gudanar da taron ne da nufin hada kai wajen tunkarar gwamnatin shugaba Assad, ta yadda za su yi waje da shi.

Dubban mutane dai aka kashe a kasar ta Syria, tun bayan da aka fara jerin zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin shugaba Assad a cikin watan Fabrairu.

Karin bayani