An kai hari a yankin Tafawa Balewa na Jihar Bauchi

Rahotanni a Nijeriya na cewa dubban mutane ne ke tserewa daga gidajensu a jihohin Benue da Nasarawa saboda fargabar tashin hankali.

Hukumomi sun ce yanzu haka an kafa sansanoinin 'yan gudun hijira guda biyu a yankin.

Hakan ya biyo bayan jerin tashe-tashen hankula ne tsakanin makiyaya da manoma a jihohin na Benue da Nasarawa.

Rikici na baya-bayan nan dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla takwas.

Wasu rahotannin kuma daga jihar Bauchi na cewa wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kai wani hari a jiya da dare a yankin Tafawa Balewa.

Dama dai yankin yana yawan fama da rikicie rikicen da ake dangantawa da kabilanci da addini .

An bayar da rahoton cewar an kona gidaje da dama tare da jikkata kananan yara a rikicin na baya bayan nan.

Karin bayani