Sojin Amurka sun mika 'Sansanin Nasara' a Iraqi

Camp Victory - ko kuma 'sansanin nasara' da Hausa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Camp Victory - ko kuma 'sansanin nasara' da Hausa

Sojin Amurka sun mika ikon tsohuwar hedikwatarsu a Iraki ga hukumomin Iraqin, a wani bangare na yunkurin da sojin Amurkar suke yi na janyewa daga kasar zuwa karshen shekara.

Sansanin na Camp Victory, ko kuma Sansanin Nasara, an kafa shi a katafariyar Fadar da Marigayi Saddam Hussain ya gina a kusa da filin jirgin saman birnin Bagdaza.

Camp Victory - ko kuma 'sansanin nasara' da Hausa - yana daya daga cikin mahimman wuraren da ke nuni da ikon Amirka a kasar Iraki.

A lokacin da sansanin ke tashe, ya kasance kusan kamar wani birni na dabam, inda ma'aikata duba arba'in da shidda ke zaune.

A nan ne kuma Amirkawa suka tsare tsohon shugaban Irakin, Saddam Hussein, bayan da aka kama shi.

An rufe Camp Victory ne, a daidai lokacin da sojan Amirka ke gab da kammala shirin janyewa daga sansanonin su, a dukan fadin kasar ta Iraki.

Karin bayani