Ana taron neman zaman lafiya a arewacin Najeriya

jami'an tsaro a Najeriya Hakkin mallakar hoto 1
Image caption jami'an tsaro a Najeriya

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta ACF ta soma wani taro a yau a Kaduna.

Suna taron ne domin duba abubuwan da ke haddasa rikice-rikice a yankin, da kuma duba hanyoyin magance su.

Manyan masu fada-a-ji na yankin da dama ne dai suka halarci ranar farko ta taron, inda da yawa suka nuna damuwa dangane da halin da ake ciki a arewacin Najeriyar.

Wasu daga cikin matsalolin da aka bayyana suna damun jama'ar yankin, musamman ma matasa, sun hada da rashin ilmi da rashin aikin yi.

An nuni a kan cewa wasu wasu 'yan siyasa a yankin suna rura wutar tashe-tashen hankula.