An gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi

zabe a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption zabe a Nijeriya

A Najeriya, Hukumar zaben kasar ta gudanar da zaben Gwamna a jihar Kogi da ke arewacin kasar.

Gabannin fara zaben dai, an yi ta bayyana fargaba game da barkewa rikici da yiwuwar tabka magudi a wasu yankunan jihar.

An dai girke jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda cikin shirin ko-ta-kwana a sassa daban daban na jihar.

Rahotannin daga jihar sun nuna cewa an gudanar da zaben cikin lumana.

Mataimakin kakakin hukumar zaben ta kasa, Mr Nick Dazang ya musanta zargin da 'yan adawa suka yi cewa akwai hadin baki tsakanin hukumar da gwamnatin jihar domin tafka magudi.

Mutane goma sha tara ne ke takarar mukamin gwamnan jihar ta Kogi.