Za a rage yawan laifukan da ake tuhumar Mr. Mladic ya aikata

Ratko Mladic Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kotu na shirin gaggauta yankewa Mladic hukunci saboda rashin lafiyar sa

Kotun duniya mai hukunta miyagun laifuka dake shari'ar tsohon kwamandan Sabiyawan Bosnia Ratko Mladic, ta amince da rage yawan laifukan da ake tuhumar Mr. Mladic din da aikatawa saboda a gaggauta yi masa shari'a.

Za a tuhumi Ratko Mladic ne akan laifuka goma sha daya- harda kisan kare dangi, kuma hakan na nufin dai an rage kusan rabin abubuwan da ake tuhumarsa akai..

Masu shigar da kara a Hague ne suka bukaci ayi hakan saboda rashin lafiyar Mr. Mladic na kara tsananta.

Daya daga cikin abubuwan da ake zargin sa da aikatawa dai shine bada umarnin kashe dubban musulmi a shekarar 1995.

Karin bayani