Serbia da Kosovo za su warware matsalar iyakokin su

Iyakar Kasashen Serbia da Kosovo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An jima ana takaddama akan iyakokin Kasashen Serbia da Kosovo

Kungiyar tarrayar Turai-EU ta ce Serbia da Kosovo sun amince da yin aiki tare dangane da kan iyokokin kasashen biyu da ake ta takaddama akai, wanda kuma shine daya daga cikin abubuwan daya raba su.

Kosovo dai ta ayyana 'yancin kanta a shekara ta 2008 amma Serbia bata amince da hakan ba.

Wannan yarjejeniyar na zuwa ne kwanaki biyar bayan da aka raunata sojojin NATO a wani tashin hankali na kabilanci tsakanin Sabiyawan dake kudancin Kosovo wadanda ke adawa da masu gadin da gwamnatin Kosovo ta aika.

Kasashen biyu dai sun amince da batun tsaro na hadin gwiwa, a tattaunawar da Kungiyar EU ta jagoranta, wanda kuma shine daya daga cikin abubuwan zai iya baiwa Serbia damar shiga cikin Kungiyar Tarrayar Turai.

Karin bayani