Austrailiya za ta fara siyarwa Indiya Uranium

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fira Ministan Austrailia, Julia Gillard

Jam'iyya mai mulki ta Labour a kasar Austrailiya ta kada kuri'a domin dage dakatarwar da ta yi na siyarwa kasar Indiya makamashin Uranium, bayan wata muhara da ta tafka.

Jam'iyyar dai ta dauki wannan matakin ne a wani tauron sauye sauye na kasa da ta gudanar.

Duk da cewa da kasar Austrialia na siyarwa kasashe kamar su China da Japan da Taiwa da kuma Amurka makamashin na Uranium, kasar ta ce ta ki siyarwa Indiya ne a baya saboda bata cikin kasashen da su ka sa hannu a dokar kasa da kasa na hana yaduwar makaman Nukiliya.

Amma wani Minista a kasar ya ce babban kuskure ne kasar ta yi na amincewa da siyarwa da Indiya, makamashin na Uranium ganin irin hadarin nukiliyar da ya faru a cibiyar fukushima dake Japan.

Jam'iyya mai mulki ta Labour a kasar Austrailiya ta amince da gwamnatin kasar da ta rika siyarwa Indiya makamashin Uranium, a wata tattaunawa kan wata yarjejeniya game da makamashin nukiliya da kasashen biyu ke yi.

Dangantaka

A baya dai dagantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu saboda matakin da Austrailiya ta dauka na kin siyarwa da Indiya Uranium.

Tun a watan Nuwamba ne dai, Pira Ministan Austrialiya, Julia Gillard ta bayyana aniyar gwamnatin ta na dage dakatarwar da ta yi na siyarwa Indiya Uranium, amma ta ce tana bukatar amincewar jam'iyyar ta.

An dai samu dan hayaniya a lokacin kada kuri'ar, inda wasu daga cikin 'ya 'yan jam'iyyar su ke ta kuwar rashin amincewa da matakin.

Amma kasar ta dau wannan matakin ne ganin cewa kasar Amurka da sauran kasashen masu makamashin na Uranium na siyarwa da Indiya, kuma idan ba ta bi sahu ba za'a bar ta a baya.

Gwamnatin kasar dai ta yi imanin duk da cewa Indiya ba ta sa hannu a dokar hana yaduwar makamin nukiliya ba, za ta iya bada tabbacin cewa Indiya za ta sarrafa makamashin na Uranium ne wajen gina abubuwan more rayuwa a maimakon makamai.