Ana zaben 'yan majalisu a Rasha

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu kada kuri'a a Rasha

Jama'a a Rasha na zaben 'yan Majalisun karamar Majalisa wadda ake kira Duma. 'Yan majalisun dai za su yi aiki a majalisar ne na tsawon shekaru biyar.

Jam'iyyu bakwai ne dai su ka fito da 'yan takara.

Tun kafin zaben dai wasu sun yi korafin cewa an keta dokar zabe.

A watan Maris din badi ne dai za'a gudanar da zaben shugaban kasa.

Gwamnatin kasar Rasha dai ta ce ta kammala shirye shiryen domin gudanar da zaben mai adalci saboda a cewar ta mulki na hannun jama'a.

Amma anyi zargin cewa 'ya 'yan karamar Majalisa wadda da ta shude 'yan amshin shatan gwamnati ne.

Abun da kuma ya sa 'yan kasar da dama ba su da kwarin gwiwa game da zaben da za'a gudanar.

A Majalisar da ta shude, Jam'iyyar Vladimir Putin ce ke da kashi biyu cikin uku na yawan kujeru a Majalisar.

Wasu dai na ganin wannan zabe wani zakaran gwajin dafi ne na gwada tasiri da Mistan Putin zai yi a zaben shugaban kasa da ke tafe a watan Maris din badi.

Har wa yau, Amurka dai ta soki yadda ake gudanarda da zaben, musamman ma yadda ake cin zarafin masu sa'ido a harkar zabe.

An dai tsare Shugabar kungiyar Golos mai sa ido a harkokin zabe a kasar na tsawon sa'o'i a filin saukar jiragen sama na Moscow a yayinda aka kwace kumfutar ta.