Herman Cain ya dakatar da takara

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Herman Cain

Dan takarar shugabancin kasar Amurka Herman Cain, ya dakatar da takarar da ya ke yi a karkashin jamiyyar Republican, wanda za a yi a badi.

Mista Cain ya shaidawa magoya bayansa a Atlanta cewa ya janye takarar ta sa ce saboda, karairayinda ake yadawa wai ya na lalata da mata.

Ya ce zargin da ake yi masa, ya yi iyalansa ciwo, sannan ya haddasa wata rashin yarda a tsakaninsa da mutanen dake tare da shi.

Daya daga cikin masu yakin neman zaben Mr Cain Steve Grubbs ya ce bai rasa aiki ba, amma ya rasa dan takara wanda abin takaici ne.

Mista Grubbs ya ce mutum ne wanda ya shafe shekaru 40 yana farfado da kamfanonin da suka doshi durkushewa, kuma ya yi imanin zai iya farfado da tattalin arzikin Amurka da ya lalace.