An gurfanar da Laurent Gbagbo a kotun duniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsohon Shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo a inda ake tsare da shi.

Tshohon shugaban Kot Dibuwa, Laurent Gbagbo, ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.

Gbagbo ya kasance shugaba na farko da ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniyar.

Ana tuhumar sa ne da laifukan da suka jibanci zubda jinin da ya biyo bayan zabukan da aka yi a kasar sa ta Ivory Coast.

Laurent Gbagbo ya bayyana ne dazu a gaban kotun ne cikin kwat da tai yana tabbatar da sunan sa ga alkalan kotun.

Sai dai ya ce gurfanarwar tasa ta keta doka.

Mutane kusan dubu uku ne dai aka kashe a kasar ta Kot Dibuwa, Laurent Gbagbo, ya ki mika mulki ga Alasane Ouattara wanda ya lashe zaben da aka yi a kasar.

Wakiliyar BBC a Hague Anna Holligan, ta tambayi babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Luis Moreno Ocampo, ko kotun na da hurumin gurfanar da Gbagbo ganin cewa tsohon shugaban kasa ne.

Mista Ocampo cewa ya yi. "Wani abun mahimmanci a nan shi ne yadda aka tsara kotun hukunta manya laifuka a duniya. Idan aka samu shugaban kasa ya aikata laifi, kotun za ta hukunta shi.

"Dokar kotun ta ce shugabannin kasashen duniya ba su da kariya.

Wannan ya sa duk shugaban kasar da ya aikata laifi sai mun gurfanar da shi, kuma Gbagbo ne babban misali."

"A watan disamban shekarar da ta gabata, mun gargadi bangarorin biyu da cewa duk wanda ya ci zarafin bil'adama domin ya samu mulki sai mun hukunta shi. Kuma a yanzu haka muna cika alkarin da muka dauka ne." In ji Luis Moreno Ocampo.

Karin bayani