Italiya da Ireland za su tsuke bakin aljihu

Pira Ministan Italiya, Mario Monti

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Pira Ministan Italiya, Mario Monti

Kasashe biyu na tarayyar turai da matsalar kudi ta yi masu katutu, wato Italiya da kasar Ireland, sun fara shirin daukar tsauraran matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

Majalisar zartarwa kasar Italiya ta amince da wasu jerin sabbin matakan karin haraji da rage kashe kudin gwamnati.

Ana sa ran Pira Ministan kasar Mario Monti, zai gabatar da shirin a gaban majalisar dokokin kasar a yau alhamis.

A Lokacin da Pira Ministan ke jawabi ga kungiyoyin kwadago ya ce gwamnati ta samu kwarin gwiwa daga shugaban kasa da majalisar dokoki, a kan hurumin daukar tsauraran matakai, da za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Shi kuwa Pira Ministan Ireland Enda Kenny cewa yayi, alummar kasa su yi shirin fuskantar tsattsauran kasafin kudi a wannan mako.