An kashe masu ibada fiye da hamsin a Kabul

Wata mata a kidime, bayan harin da aka kai a Kabul Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wata mata a kidime, bayan harin da aka kai a Kabul

'Yan sanda a Afghanistan sun ce wani dan kunar bakin wake ya kashe sama da masu ibada hamsin, a wajen wani ibada dake birnin Kabul a lokacin da 'yan Shi'a ke bikin ranar Ashura.

Tashin hankalin, wanda ya raunata wasu karin mutanen dari daya, ya faru ne a lokacin da Musulmai 'yan Shi'a ke taruwa domin bikin ranar Ashura, wadda ta kasance ranar hutu a Afghanistan.

Wakilin BBC a Kabul ya ce ba'a taba kai irin wannan harin Haula ba a Afghanistan.

Shugaba Hamid Karzai ya ce wannan shi ne karon farko da aka taba kai irin wannan harin ta'addanci a rana mai tsarki a kasar ta Afghanistan.

Mayakan Taliban dai sun ce ba su da hannu wajen kai wannan hari.

Karin bayani