'Da wuya a samu zaman lafiya a arewa'- Bafarawa

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Tsohon, gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarwa

A Najeriya tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya ce da wuya a samu zaman lafiya arewacin kasar, muddin shugabanni a yankin ba su maida hankali wajen kyautata rayuwar al`umomin jihohinsu ba.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a dai-dai lokacin da kungiyar dattawan arewa ke wani taron a kan zaman lafiya a yankin

A cewar Bafarawa, taron dogon turanci ne kawai maras amfani.

A wata tattaunawar da ya yi da Wakilin BBC, tsohon Gwaman ya ce an gayyace shi taron amma bai je ba, saboda an kauce wa manufofin kungiyar.

Ya ce; "Wannan kungiya an kafa ta ne domin ci gaban arewa ta hanyar siyasa da illimi da kuma hanyar noma.

"Idan aka duba kafuwar kungiyar ya zuwa yanzu babu abun da ta cimma kusa shekaru goma kenan."

Ya ce kungiyar ta kaucewa akidar ta da ta kira taron zaman lafiya.

Alhaji Bafara ya ce: "In maganar zaman lafiya ne, ba sau an hadu Kaduna ba, domin zaman Kaduna turanci ne kawai.

"Hakkin mu na kowa ya zauna ayi nazarin yadda za'a Inganta rayuwar al'umma.

"Babbu yadda za'a samu zaman lafiya, idan ana fama da yunwa." In ji Attahiru Bafarawa.

Karin bayani