Ana sauraran sakamakon zabe a Congo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana sauran sakamakon zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Hukumar zabe a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na shirin fitar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a makon da ya gabata.

Jam'iyyar Shugaban kasa mai ci, Joseph Kabila ce ke kan gaba a sakamakon farko farko da ake fitarwa, amma 'yan adawa a kasar sun yi gargadin cewa ba za su amince da zaben ba.

Shugaban Hukumar zaben Congo ya ce, yana kokarin ya ga ya cimma wa'adin da ake diba na fitar da sakamakon wanda kuma zai cika a yau dinan.

A yau ne dai za'a bayyana sabon shugaban kasar, idan dai duk cibiyoyin zabe a kasar sun fito da sakamakon zabukan da aka gudanar a yankunansu.

Ana dai kokarin a fito da sakamon zaben ne kafin wa'adin shugaban kasa mai ci a yanzu, wato Joseph Kabila ya cika.

Kusan kashi biyu cikin uku na sakamakon da aka fitar a ranar Litinin ya nuna cewa Mista Kabila ne a kan gaba.

Amma abokin takararsa, Etienne Tshisekedi na ikirarin cewa shine ya yi nasara.

Tuni dai jami'an tsaro su ke cikin shirin ko ta kwana, bayan rikicin da akai ta yi tsakanin magoya bayan bangarorin biyu a makon daya gabata.