An jinkirta bayyana sakamakon zabe a Congo

Image caption Ma'aikatan hukumar zabe na tattara sakamako

Hukumar zaben Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta bada sanarwar dalilanta na kasa bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a makon jiya da cewa sun faru ne saboda karancin kayayyakin aiki.

A karkashin kundin tsarin mulkin kasar dai, wa'adin mulkin shugaban kasar ya kare daga sha biyun daren jiya agogon kasar.

Kakakin babban dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar adawa, Etienne Tshisekedi, ya ce ba za su amince da shugabancin Joseph Kabila ba, da zarar wa'adin mulkinsa ya kare.

Mr Kabila dai shi ne ke gaba a sakamakon farko da aka bayyana.

Tuni dai jami'an tsaro su ke cikin shirin ko ta kwana, bayan rikicin da akai ta yi tsakanin magoya bayan bangarorin biyu a makon daya gabata.