Mutane shida sun mutu a Kadunan Najeriya

'Yan kwana-kwana sun kai dauki
Image caption 'Yan kwana-kwana na yunkurin kashe wutar da ta tashi bayan fashewar

Jami'an tsaro a Najeriya sun ce akalla mutane shida ne suka mutu bayan da wani abu ya fashe a garin Kaduna da ke Arewacin kasar, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Rundunar 'yan sandan jahar dai ta tabbatarwa da BBC cewa mutane 6 sun hallaka a lamarin, yayin da wasu suka samu raunuka musamman kuna.

Wasu da suka ganewa idanunsu lamarin, sun ce bamne ne ya tarwatse a wani wurin sayar da kayayyakin gyara da ke kan titin Katsina a cikin garin na Kaduna.

Amma hukumomi a jihar na cewa wasu tukwanen gas ne suka fashe.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Kaduna Bala Nasarawa, ya ce masu bincike na kokarin gano musabbabin aukuwar lamarin.

Bayanai dai sun nuna cewa wasu ne wadanda ba a san ko su wanene ba suka yi kokarin jefa wani abu a cikin wasu shagunan sayar da kayan gyaran mota, amma abin ya tashi har da su.

A cikin mutanen da suka rasa rayukansu har da wasu wadanda ke wucewa.

"Cikin wadanda lanmarin ya ritsa da su har da wani yaro dan shekaru 3, wanda tuni mahaifinsa ya karbi gawarsa domin binnewa," kamar yadda kakakin hukumar samar da agajin gaggawa ta NEMA Yushau Shuaib, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Jihar Kaduna wacce ke da jama'a mabiya addinai daban-daban ta sha fuskantar tashin hankali mai nasaba da addini da kuma kabilanci.

Ko a watannin baya an samu karar fashewar wasu bama-bamai a wasu sassan jihar.

Karin bayani