Wani abu ya fashe a birnin Kadunan Najeriya

'Yan kwana-kwana sun kai dauki
Image caption 'Yan kwana-kwana na yunkurin kashe wutar da ta tashi bayan fashewar

Wani abu wanda ake kyautata zaton bom ne ya tashi a wata unguwa wadda ake kira Oriyakwata a cikin garin Kaduna, a arewacin Najeriya, inda ya hallaka mutane da dama ya kuma jikkata karin wasu.

Bayanai dai sun nuna cewa wasu ne wadanda ba a san ko su wanene ba suka yi kokarin jefa wani abu a cikin wasu shagunan sayar da kayan gyaran mota, amma abin ya tashi har da su.

A cikin mutanen da suka rasa rayukansu har da wasu wadanda ke wucewa.

Hukumomi dai sun tabbatar da afkuwar wannan al'amari to amma sun musanta cewa abin da ya haddasa fashewar da gobarar da ta biyo baya bom ne.