'Yan sanda sun yi galaba a kan 'yan fashi

Jami'an tsaro Najeriya

Asalin hoton, google

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro Najeriya

A Najeriya, ga alama tsattsauran matakin tsaron da ake dauka musamman a manyan birane, ya sa a yanzu masu aikata miyagun laifuffuka sun fi mayar da hankali a yankunan karkara.

A irin wannan yunkurin ne wadansu 'yan fashi da makami suka kai farmaki a kan wani bankin al'umma da ke garin Batsari a jihar Katsina.

Rahoton da muka samu ya ce 'yan fashin sun bi sawun albashin ma'aikatan karamar hukumar ne wanda aka kai bankin, inda suka rika harbin kan-mai-uwa-da-wabi suka kashe wadansu mutane da jikkata wasu, yayinda kuma suka yi awon-gaba da baki-dayan albashin.

'Yan sanda sun bi 'yan fashin, sun kwaci kudin, bayan sun harbi wadansu daga cikinsu sun kuma kashe dan fashi guda.

Wakilin BBC a Katsina ya ce 'yan fashin su kimanin bakwai sun kai harin ne a bankin na al'umma da ke Batsari a kan sababbin Babura, kuma da isar su kofar bankin, kafin dan sandan da ke tsaron kofa ya ankara sun bankare shi sun kwace bindigarsa.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina, Ibrahim Mohammed, ya shaidawa BBC cewa da karfin tsiya suka kutsa kai cikin bankin suka rika harba bindigogi suka kwaci kudin.

'Yan fashin, wadanda suka rika harbi lokacin da suke kokarin tserewa, sun jikkata mutane da dama.

Nan take, baya ga mutum guda da ya rasa ransa, an kwaso kimanin mutane goma sha bakwai zuwa babban asibitin Katsina.