Amurka za ta karfafa yancin 'yan Luwadi da madugo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Gwamnatin Amurka ta ce za ta yi amfani da diflomasiyya ne wajen karfafa 'yancin 'yan luwadi da madugo a duniya.

Da ta ke jawabi a Geneva, Sakatariyar Harkokin Kasashen Waje Hillary Clinton ta ce ba laifi ba ne in mutum na son zama dan luwadi ko madugo.

Misis Clinton ta ce Amurka za ta rika la'akari da yadda kasashen ke tafiyar da batun kafin ta ba su tallafi.

Gwamnatin Amurka dai ta umarci hukumominta da su rika la'akari da yadda kasashe ke tafiyar da al'amuran 'yan luwadi da madugo kafin su san irin tallafin da za su rika bayarwa.

Har wa-yau, kasar ta ce za ta rika sa-ido sosai a kan bukatun 'yan luwadin da madugo da ke neman mafakar siyasa a Amurka.

Amurka dai ta bukaci jami'anta su rika hada kai da kungiyoyin kasa-da-kasa a duniya, domin yaki da bambance-bambancen da ake nunawa masu dabi'ar.

Wadannan abubuwan na cikin batutuwan da Hillary Clinton ta bayyana a bikin ranar 'yancin bil-Adama.

Misis Clinton ta ce fafutukar da 'yan luwadi da madugo su ke yi, daidai ta ke da fafutukar masu yaki da wariyar launin fata da kuma nuna bambancin jinsi.

Tun bayan da Shugaba Obama ya hau mulki dai, ya sauya dokar da ke hanawa 'yan luwadi da madugo shiga sojin kasar, sannan kuma ya soki dokar da kasar Uganda ta kafa wadda ta kayyade hukuncin kisa a kan masu dabi'ar.

Duk da irin wadannan matakan da gwamnatin Amurkan ta dauka, har yanzu dai tana jan kafa wajen nuna goyon baya ga auren jinsi daya a kasar.

Karin bayani