Tarayyar Turai na fuskantar hadarin rugujewa-Sarkozy

Nicolas Sarkozy Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Nicolas Sarkozy

Shugabannin Faransa da Jamus sun yi wani roko na ba zata domin samun goyon baya daga sauran kasashen tarayar turai, a yunkurin da suke yi na ceto kudin Euro, wanda basukan da wasu gwamnatoci suka ci iya wuya ke neman durkusar da shi.

Yayinda shugabannin ke hallara domin wani muhimmin taron koli na tarayyar turai ranar Jumaa, shugaba Sarkozy na Faransa ya yi gargadin cewa ba a taba fuskantar barazanar wargajewar tarayyar turan irin wannan lokaci ba.

Ita kuma shugabar gwamnatin Jamus, Angela merkel cewa ta yi akwai bukatar aiwatar da sauye sauye ga kundin tsarin mulki tarayyar turan kan batutuwan da suka shafi harkokin kudi.

Karin bayani