An bude mahadar arewa da kudancin Najeriya

Tsofaffin masu tayar da kayar baya na Naija Delta Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu daga cikin tsofaffin masu tayar da kayar bayan na Naija Delta

Jami'an tsaro a Najeriya sun yi nasarar hana wadansu tsofaffin masu tayar da kayar baya na yankin Naija Delta wadanda suka ajiye makamai shiga babban birnin kasar, Abuja.

Gamayyar jami'an tsaro a Jihar Kogi, wadda ta hada da 'yan sanda da sojoji da kuma masu farin kaya, wato SSS, sun hana su wucewa ne ta hanyar datse gadar Koton-karfe da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja, wadda ita ce daya daga cikin manyan hanyoyin da suka hada bangaren arewaci da kudancin Najeriya.

Jami`an tsaron sun kwashe sa'o'i da da dama tun kusan talatainin daren jiya, har zuwa yau, kusan karfe daya na rana, suna kokarin shawo kan masu gwagwamayar, kafin su amince su karya linzami su koma wuraren da suka fito, kana hanya ta bude.

Jami`an tsaron dai sun samu galaba ne cikin lumana bayan sun gamsar da kwambar tsofaffin masu fafutukar, kimanin mutum dari biyu bayan sun tabbatar musu cewa za a mika korafe-karafensu ga gwamnatin tarayya.

Babban korafin nasu dai shi ne zargin da suka yi cewa gwamnatin kasar ta gaza wajen cika alkawuran da ta yi na inganta musu rayuwarsu a cikin shirinta na yi musu afuwa.

Kazalika sun ce suna cike da bukatu, saboda ko abin yin bikin Kirsimata su da iyalansu ba su da shi.

Sai dai mai baiwa Shugaban Najeriya shawara a kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak, ya ce gwamnati na bakin kokarinta, kuma idan suka yi hakuri kowa zai ci gajiyar shirin.

Wannan datse hanya da jayayyar da aka yi ta yi da tsofaffin masu gwagwarmayar sun jefa masu ababen hawa da matafiya cikin mawuyacin hali, saboda baya ga katse musu tafiya, sun yi fama da rashin abinci, ga kuma zaman takura a mota na lokaci mai tsawo.

Hanyar Lokoja dai na cikin manyan hanyoyin da suka hada bangaren arewaci da kudancin Najeriya, kuma saboda muhimmancin wannan hanya gungun jama'a da dama kan yi amfani da ita wajen huce haushinsu da hukuma ta hanyar datse ta idan suna zanga-zanga.

A wadansu lokuta a baya ma ma'aikatan kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta sun sha datse hanyar yayin zanga-zangar da suka yi.

Kuma masu lura da al'amura na bayyana cewa matukar ba a samu sauyin dabi'ar datse hanyar ba to haka za a ci gaba da jefa matafiyan da ba su ji ba su gani ba cikin wahala, ba gaira ba dalili.

Karin bayani