An harbe Alfredo Landaverde na Kasar Honduras

Honduras Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An hallaka babban jami'in yaki da miyagun kwayoyi a Honduras

An harbe tsohon Shugaban hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Kasar Honduras, Alfredo Landaverde, har lahira a Tegucigalpa.

Wasu 'yan bindiga biyu kan babur da ba a tantance ko su waye ba ne suka harbe Mr. Landaverde, wanda ke tafiya a cikin motarsa tare da matarsa.

Ya dai kasance mai matukar sukar 'yansanda kan cin hanci da rashawa.

A cikin watan Oktoba, ya zargi manyan 'yansanda 25 da kasancewa a aljihun dillalan miyagun kwayoyi.

Wakilin BBC ya ce, Kasar ta fi kowace Kasa a duniya yawan aikata kisan kai, kuma tana fuskantar sabon kalubale.

Dillalan miyagun kwayoyi na Kasar Mexico na bazuwa a ko'ina cikin tsakiyar Amurka, abinda ke sa cin hanci da rashawa a cikin cibiyoyi da kuma dakarun tsaron Honduras.

Karin bayani