Vladimir Putin ya zargi Hillary Clinton

Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firayim Minista Vladimir Putin na Rasha

Firayim Minstan Rasha Vladimir Putin ya zargi Amurka da kista tashin hankalin da aka yi a kan zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar a kasarsa kwanannan.

Mista Putin ya ce sukar zaben da sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta yi, tana cewa cewa ba a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci ba, ta karfafawa masu adawa da gwamnati gwiwa har suka fito suka yi zanga-zanga.

Ya kara da cewa wadanda suke zanga-zanga a kan nasarar jam'iyyarsa ta United Russia na yin haka ne saboda bin son-zuciyarsu kawai da kuma neman cimma wata manufa ta siyasa.

"Na yi nazari a kan kalaman abokanmu, wato Amurka, abu na farko da Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka ta ce shi ne ba a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci ba, ko da yake ba ta samu rahoton wadanda suka sa ido a zaben ba, amma kalaman nata su ne suka ingiza zanga zanga", in ji Mista Putin.

Daga nan sai Mista Putin ya ce yayin da wajibi ne a mutanta 'yancin gudanar da zanga-zanga, tilas ne kuma a rika bin doka da oda.

"Game da abubuwan da suka faru a kan tituna, abin da wadansu ke kira dimokuradiyya, abin da zan ce a nan shi ne idan mutane suka bi doka, tilas ne a ba su dama su bayyana ra'ayoyinsu, kuma ba za mu takaita 'yancin kowanne mutum ba; amma idan mutum ya karya doka, tilas ne hukumomin tsaro ta kowanne hali su tabbatar cewa an bi dokokin kasa".

Mista Putin ya kuma kara da cewa akasarin 'yan kasar Rasha ba sa son ganin irin boren da aka yi a wadansu kasashe makwabta ya faru a kasar su.

"Mun san cewa al'ummomin kasar mu ba sa son abin da ke faruwa a Rasha ya kai yadda ya faru a Kyrgyzstan ko Ukraine a 'yan shekarun nan, babu wanda yake son tashin hankali", in ji shi.

Vladimir Putin ya kuma yi zargin cewa gwamnatocin wadansu kasashe na turo makuden kudade cikin kasarsa don ganin sun karkata zabubbukan kasar, sannan ya nemi a samar da dokoki masu tsauri don hukunta 'yan asalin kasar Rasha da ke aiki da wadansu gwamnatocin kasashen waje da nufin ganin sun yi tasiri a harkokin siyasar kasar Rasha.

Karin bayani