Tshisekedi ya yi watsi da sakamakon zaben Congo

Etienne Tshisekedi Hakkin mallakar hoto
Image caption Etienne Tshisekedi

Dan takarar Babbar jam'iyyar adawa a Jumhuriyar Demokradiyyar Congo, ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da Hukumar zabe ta bayyana, wanda ya nuna cewa shugaba mai ci yanzu, Joseph Kabila ne ya lashe zaben.

Etienne Tshisekedi ya ce yana daukan kansa a matsayin zababben shugaban kasar, yana mai cewa bayyana Mr Kabila a matsayin wanda ya lashe, wata takala ce.

Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a Kinshasa, babban birnin kasar, saboda fargabar da ake da ita, ta barkewar tashin hankali, bayan bayyana sakamakon zaben.

Wani wakilin BBC a birnin ya ce an ji karar harbin bindigogi, kusa da gidan Mr Tshisekedi.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce masu zanga-zanga sun kona tayoyi tare da yin jifa da duwatsu a kan 'yan sanda a kusa da tsakiyar birnin.

Sakamakon wucin gadi na zaben dai ya nuna cewa shugaba Kabila ya samu kashi 49 cikin 100 na kuru'un da aka kada, yayinda Mr Tshisekedi ya samu kashi 32 daga cikin 100.

Yanzu ya rage kotun kolin kasar ta tabbatar da sakamakon zaben.

Karin bayani