Kungiyar tarayyar Turai ta samu nasara

Kungiyar tarayyar Turai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar tarayyar Turai

Dukkanin kasashen tarayyar Turai, banda Burtaniya, sun goyi bayan wata yarjejeniya da suke saran zata maida kimar yankin Turan dake amfani da kudin Euro wanda ke fama da matsalar bashi.

Amma kuma yarjejeniyar bazata zama cikakkiyar yarjejeniya da zata yi aiki a duk Turai ba saboda Burtaniya taki amince wa da ita.

Wani mai magan da yawun shugaban majalisar Tarayyar Turan , VAN RUMPOY na ganin cewa anyi nasara duk da rashin jituwar da aka samu.

Inda yace abu muhimmi shine tabbatarda daidaito, da kuma makoma mai kyau ga kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Kuma irin wadannan bambamce bambamce da ake samu abu ne mai mai kyau.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce shugabannin kasashen Turai sun dauki babban matakin daidaita al'amura a yankin.

Karin bayani