Gobara ta cinye wani asibiti a birnin Kolkata na India

Gobara a India Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gobara ta cinye wani asibiti a India

Wata gobara ta cinye wani asibiti a birnin Kolkata na India, kuma jami'ai sunce su na jin kusan mutane 20 ne suka hallaka.

'Yan kwana-kwana sun fasa bangayen gilasai na asibitin, sannan su ka yi amfani da kwarangar igiya domin cetar majinyatan da aka rutsa da su hawa na sama na ginin.

Sun kuma kwashe sa'o'i da yawa kafin su kashe gobarar.

Minista mai kula da Jihar Yammacin Bengal ya ce har yanzu ba a san abinda ya haddasa gobarar ba.

Karin bayani