Ban Ki Moon a Somalia

Ban Ki Moon a Somalia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ban Ki Moon a Somalia

Sakatare janar na Majalisar Dinkin DUNIYA, Banki Moon na wata ziyara a Mogadishu babban birnin Somalia.

Shine jami'i mafi girman mukami da zai ziyarci kasar a cikin shekaru dadama.

Wakilin BBC yace Mr Ban ya sauka a filin jirgin saman kasar ne sanye da rigar sulke, kuma Praministan Somalia ne ya tarbi shi, kana ya yi masa jagora zuwa fadar shugaban kasar.

Kungiyar masu tsatsauran ra'ayin Islama ta Alshababba dai na yawan kai hare hare a babban birnin kasar, amma a 'yan watannin baya bayannan an fattake su daga Mogadishu, kuma hakan nema ya sa Mr. Ban ya iya kai wannan ziyarar.

Karin bayani