Za a gudanar da gagarumar zanga-zanga a Rasha

Zanga-zanga a Rasha Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana tsammanin gudanar da gagarumar zanga-zanga a Rasha yau asabar

Wata cibiyar kare hakkin bil-adama da aka kafa a Rasha domin baiwa Shugaba Dmitry Medvedev shawara ta ce, ya kamata a sake zaben 'yan majalisar dokokin Kasar matukar aka tabbatar da zarge-zargen magudi a zaben da ya gabata.

Cibiyar wadda ba ta da ikon tilasta sake zaben, ta ce rahotannin magudin zaben abin damuwa ne, kuma ya kamata a hukunta wadanda suka aikata laifi.

Dubun-dubatar jama'a ne dai ake sa ran za su gudanar da zanga-zanga a birane da dama na Kasar Rashan a yau Asabar, inda za su yi kiran a sake zaben.

Rashid Nurgaliyev, shi ne ministan cikin gida na Kasar ta Rasha, ya kuma yi kira ga masu zanga-zangar da kada su karya doka.

Karin bayani