Turkiyya ta gargadi Syria

Firayim Ministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Turkiyya tace rikicin Syia na yin barazana ga zaman lafiyar yankin

Turkiyya ta yi gargadin cewa, ba za ta zura ido tana kallon amfani da karfin da Kasar Syria ke yi wajen murkushe masu zanga-zanga ya haifar da hadari ga zaman lafiyar yankin ba.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu, ya ce alhaki ne a kan Turkiyya ta ce ya isa haka idan ta ga gwamnatin da take yakar mutanen ta tana barazana ga tsaronta.

A gefe daya kuma tsohon babban jami'in tsaron Saudiya Yarima Turki al-Faisal, ya ce ya yi amannar cewa Kasashen larabawa ba za su bari a ci gaba da kisan gilla ga 'yan Kasar Syria ba.

A nata bangaren, Kasar Syria ta yi kira ga Kasashen duniya da su taimaka mata wajen samun mafita a rikicin.

Karin bayani