Jacob Zuma na Ziyara a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaba Jabcon Zuma na Afrika ta Kudu na ziyarar aiki a Najeriya inda ya tattauna da shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan kan wasu al'amura da suka shafi hadin kan nahiyar Afrika.

Shugabannin biyu sun kuma ce wajibi ne shugabannin Afrika su dauki matsaya guda kan duk wasu al'amura da suke ci wa nahiyar tuwo a kwarya, sannan su yi aiki tare domin tabbatar da muradun kungiyar Tarayyar Afrika.

Sun kuma nanata cewa dole ne su kara kaimi wajen tabbatar da cewa matakan da shugabannin Afrika suka dauka karkashin kungiyar Tarayyar ta Afrika an aiwatar da su sau-da-kafa.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce wajibi ne kasashen Afrika su rinka magana da murya guda.

"Bai kamata a ce tarayyar Afrika kawai ta na fadar matsayarta ba ne kan al'amuran da suka shafi yankin - ba tare da aiwatarwa ba - wato irin abinda Hausawa ke cewa fada ba cikawa".

Tunawa da marigayi Yar'adua

Shugaba Zuma ya kuma halarci taron tunawa da marigayi Shehu Musa Yar'adua inda ya kasance babban bako na musamman.

"Wajibi ne kasashen Afrika su tashi tsaye domin shawo kan matsalolinsu domin kaucewa mamayar kasashen duniya da kuma irin cin mutuncin da aka yiwa marigayi Kanal Mu'ammar Gaddafi na Libya," a cewar Zuma.

Jacob Zuma zai kuma halarci wani biki a jami'ar Amurka da ke jihar Adamawa, inda za a bashi digirin girmamawa.

Wannan ziyara na da muhimmanci ta fannoni da dama ga kasashen biyu, kuma wannan ne ya sa ma shugabannin suka yi bitar yadda lamarua suke a haniyar ta Afrika kafin babban taron kungiyar tarayyar Afrika da za a yi.

Suka ce ya kamata taron ya magance matsalolin da ake fuskanta a kasashen Libya da Cote D'Ivoire da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

Karin bayani