Shugaba Kabila ya ce an yi kura-kurai a zaben kasar

Hakkin mallakar hoto

Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Joseph Kabila ya amsa cewar an tafka kura-kurai zaben shugaban kasar na watan jiya.

A wani taron manema labaru a babban birnin kasar Kinshasa, shugaba Joseph Kabila ya ce sun so su shirya sahihin zabe amma hakarsu ba ta cinma ruwa ba.

Sai dai ya yi watsi da sakamakon da masu sa ido na kasashen duniya suka fitar na cibiyar Carter, wanda ke nuna cewar zaben ba shi da wata kima.

Cibiyar Carter ta ce an batar da sakamakon zabe daga mazabu kusan dubu biyu a Kinshasa, babban birnin kasar. Sakamakon wucingadi da aka fitar ya nuna cewa Mr Kabila ne yayi nasara a zaben, amma nan da nan jagoran 'yan adawa, Etienne Tshisekedi yayi watsi da sakamakonsa tare da ayyana kansa a matsayin shugaban kasa

Karin bayani