Jama'a basu fito sosai ba a zaben Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto AFP

An rufe rumfunan zabe a yinin farko na zaben 'yan majalisar dokoki a Ivory Coast, wanda shi ne zaben farko tun bayan zaben shugaban kasar da ya haddasa rikicin siyasar kasar.

Jam'iyyar Laurent Gbagbo, tsohon shugaban kasar tana kaurace wa zaben.

Kin saukarsa daga kan mulki bayan zaben shugaban kasa a bara ya jawo mummunan zubar da jini a kasar.

'yan jami'yyar sun yi kukan ana musguna masu, kuma hukumomin zabe suna fifita jam'iyyar Shugaba Alassane Ouattara.

An dai kai Mr. Gbagbo kotun hukunta laifukan yaki da ke Hague don fuskantar tuhumar aikata laifukan cin zarafin bil'adama.

Daruruwan magoya bayansa ne dai suka yi zanga-zanga a harabar kotun don nuna adawar su da shari'ar da ake yi masa.

Karin bayani