An samu girgizar kasa mai karfi a Mexico

Shugaba Felipe Calderon na Mexico Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Girgizar kasa a Mexico ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu

Wata girgizar kasa mai karfi ta auka wa wani yanki na kudu maso yammacin Kasar Mexico, inda ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane biyu.

Ta kuma girgiza gine-gine a Mexico City babban birnin Kasar inda mutanen da suka firgita suka fice a guje zuwa kan tituna.

Wakilin BBC yace wannan na daga cikin girgizar kasa mafi karfi da ta shafi mexico city a cikin shekaru da dama.

An dai samu wasu kananan girgizar kasar da suka biyo baya a babban birnin kasar.

Babbar girgizar kasar dai ta auku ne a jihar Guerrero.

Karin bayani