An sake gurfanar da Sanata Ndume a Kotu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

An gurfanar da dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, a gaban wata babbar kotu a Abuja a bisa zargin aikata laifuka huddu da suka shafi ta'addanci, da kuma bayyana sirrin kasa ba bisa ka'ida ba.

Sanatan dai ya musanta aikata laifin.

Kotun dai ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Sanata Ndume, bayan da lauyoyin wadanda suka shiga da karar suka bukaci hakan.

Da fari dai lauyoyin Sanatan sun nemi kotun da ta ba da shi beli, sai dai hakan bai yiwu ba saboda korafin da lauyoyin wadanda suka shigar da karar suka yi cewa, ba a sanar da su game da bukatar neman beli a kan lokaci ba.

Hukumar leken asirin Najeriya ce dai ta kama Sanata Ndume a watan jiya, tare da Umar Sanda Koduga, wanda ta zarge shi da kasancewa kakakin kungiyar Boko Haram.

Tuni dai Umar Sanda Konduga ya amsa laifinsa kuma har an yanke masa hukunci