Pakistan ta ce ta na zaman doya da manja ne da Amurka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Firaministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani, ya ce kasar sa ba ta amince da Amurka ba, haka ita ma Amurka.

Ya ce akwai gibi game da amincewa da juna, ana dai aiki tare be amma ba'a yarda da juna ba. Firaminista Gilani ya ce za a dauki makwanni kafin Pakistan ta janye datse hanyar da ta yi wa ayarin motocin da ke dauke da kayayyaki zuwa dakarun NATO a Afghanistan. Dangantakar kasashen biyu ta yi tsami ne bayan sojin Amurka suka kashe sojin Pakistan da ke tsaron hanya guda ashirin da hudu a wani hari ta sama.

Karin bayani